Ɓangaren Gwamna Abudllahi Umar Ganduje ya yi nasara a ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da wata kotun ta bai wa ɓangaren tshohon Gwamna Ibrahim Shekarau a rikicin jam'iyyar APC mai mulkin Jihar Kano.
Ɓangaren Gwamna Abudllahi Umar Ganduje ya yi nasara a ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da wata kotun ta bai wa ɓangaren tshohon Gwamna Ibrahim Shekarau a rikicin jam'iyyar APC mai mulkin Jihar Kano
A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta yi ba daidai ba ne sannan ta tabbatar da cewa shugabannin da ɓangaren Ganduje ya zaɓa su ne halastattu.
Hukuncin kotun na yau ya bai wa ɓangaren Ganduje nasara a duka ɓangarori ukun da suka ɗaukaka ƙarar a kan su, kamar yadda Barista Abdullahi Adamu Fagge ya shaida BBC Hausa - ɗaya daga cikin lauyoyin ɓangaren gwamna.
Tun farko, ɓangaren da Shekarau ke jagoranta ya shigar da uwar jam'iyyar ƙara da kwamatin shugbancinta na ƙasa da kuma sakatarenta a ɓangare ɗaya, sannan suka shigar da shugabancin APC na Kano a ɗaya ɓangaren, da kuma kwamatin da ya shirya zaɓen shugabancin jam'iyyar a Kano a wani ɓangaren daban.
A zaɓen da aka gudanar mai cike da rarrabuwar kai a watan Nuwamban 2021, ɓangaren Shekarau ya zaɓi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban APC na jiha yayin tsagin Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas.
A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam'iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.
Sai dai ya yi wuri a iya bayyana abin da hukuncin ke nufi ga APC a jam'iyyance musamman ganin yadda ake tunkarar babban zaɓe na 2023.
Commentaires
Enregistrer un commentaire