Articles

Ukraine ta ce mutum bakwai sun rasu a harin bam ɗin da Rasha ta kai mata

Image
  Ukraine ta ce mutum bakwai sun rasu a harin bam ɗin da Rasha ta kai mata Reuters Copyright: Reuters Aƙalla mutum bakwai aka sanar da mutuwarsu a wani harin bam da dakarun Rasha suka kai a Ukraine, kamar yadda ƴan sanda a Ukraine ɗin suka sanar. Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa wani hari da aka kai wani sansanin soji da ke a Podilsk a wajen Odessa ya yi sanadin mutuwar mutum shida da kuma raunata mutum bakwai. Haka kuma akwai mutum 19 da ba a san inda suke ba. Haka kuma an tabbatar da cewa mutum guda ya rasu a birnin Mariupol.

Ɓangaren Gwamna Abudllahi Umar Ganduje ya yi nasara a ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da wata kotun ta bai wa ɓangaren tshohon Gwamna Ibrahim Shekarau a rikicin jam'iyyar APC mai mulkin Jihar Kano.

Image
  Ɓangaren Gwamna Abudllahi Umar Ganduje ya yi nasara a ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da wata kotun ta bai wa ɓangaren tshohon Gwamna Ibrahim Shekarau a rikicin jam'iyyar APC mai mulkin Jihar Kano . Yanda zakaga application da yafi cima lokaci / Damu daku TV https://www.youtube.com/watch?v=9MQuw0R1rbw A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta yi ba daidai ba ne sannan ta tabbatar da cewa shugabannin da ɓangaren Ganduje ya zaɓa su ne halastattu. Hukuncin kotun na yau ya bai wa ɓangaren Ganduje nasara a duka ɓangarori ukun da suka ɗaukaka ƙarar a kan su, kamar yadda Barista Abdullahi Adamu Fagge ya shaida BBC Hausa - ɗaya daga cikin lauyoyin ɓangaren gwamna. Tun farko, ɓangaren da Shekarau ke jagoranta ya shigar da uwar jam'iyyar ƙara da kwamatin shugbancinta na ƙasa da kuma sakatarenta a ɓangare ɗaya, sannan suka shigar da shugabancin APC na Kano a ɗaya ɓangaren, da kuma kwamatin da ya shirya zaɓen shugabancin...