Ukraine ta ce mutum bakwai sun rasu a harin bam ɗin da Rasha ta kai mata



 Ukraine ta ce mutum bakwai sun rasu a harin bam ɗin da Rasha ta kai mata

.

Aƙalla mutum bakwai aka sanar da mutuwarsu a wani harin bam da dakarun Rasha suka kai a Ukraine, kamar yadda ƴan sanda a Ukraine ɗin suka sanar.

Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa wani hari da aka kai wani sansanin soji da ke a Podilsk a wajen Odessa ya yi sanadin mutuwar mutum shida da kuma raunata mutum bakwai.

Haka kuma akwai mutum 19 da ba a san inda suke ba.

Haka kuma an tabbatar da cewa mutum guda ya rasu a birnin Mariupol.

Commentaires